Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin neman umarnin hana Hukumar ICPC, da sauran hukumomi daskarar da asusunsa na banki ko ƙwace kadarorinsa.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan kotun ta amince da hujjar cewa shigar da ƙarar ya zama amfani da tsarin kotu ta hanyar da ba ta dace ba, musamman ganin cewa El-Rufai ya riga ya shigar da wasu ƙararraki masu alaƙa da wannan batu a wasu kotuna.
El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a kan ICPC, EFCC da DSS, da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ya nemi kotun ta hana hukumomin ɗaukar matakin daskarar da asusunsa ko ƙwace kadarorinsa, yana mai cewa kuɗin sallamar da ya samu bayan barin kujerar gwamnan Kaduna tsakanin shekarar 2015 da 2023 halal ne.
A nata ɓangaren, ICPC ta yi gardamar cewa ƙarar tana da alaƙa da binciken laifi da take gudanarwa, kuma shigar da ƙararraki masu kama da juna a kotuna daban-daban na iya haifar da hukunci masu saɓani. Kotun ta kuma bayyana cewa ba za a yi amfani da tsarin shari’a wajen hana hukumomin bincike gudanar da ayyukan da doka ta ba su ikon yi ba.
Sai dai wannan hukunci na watsi da ƙarar ba ya nufin cewa an tabbatar da laifi a kan El-Rufai; batu ne da ya shafi ƙarar da ya shigar da kuma dalilan kotu na yin watsi da ita.
