Tsohon gwamnan ya yi kakkausar suka ga ‘yansanda ne kan barazanar tsaro da suka sanar don hana taron mauludi da sarkin Kano ke jagoranta.
Kwankwaso ya bayyana abin da rundunar ‘yan sandan ta yi da cewa ya kaucewa tsarin gudanar da aikinsu kuma wanda bai kamata ba.
Tsohon Sanatan ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta na X a ranar Litinin.
Yana mai cewa, sanarwar da rundunar ta fitar ya haifar da tsoro da kuma firgici a zukatan al’ummar jihar da kuma dubban bakin da suka zo daga cikin da kuma wajen Najeriya.
“Hakan ya batawa rundunar suna da kima da kuma darajar da jama’a ke kallon ta da su wanda kuma ba karamin koma baya ba ne ga sha’anin tsaro a jihar da kuma kasa baki daya.
“Hakika fitar da sanarwar tsaro irin wannan na karya babban hadari ne, kuma saka ne da mugun zare wanda zai sa mutane su yi watsi da irin wannan sanarwa na hakika nan gaba idan rundunar ta yi.” Inji shi.
Jagorar na siyasar kwankwasiyya ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daina tsoma baki a al’amuran cikin gida na jihar wanda hurumi ne na gwamnatin jihar wacce jama’ar suka zaba.
A ranar Juma’a ne jami’an ‘yansansdan suka yi wa filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata kawanya domin hana taron Mauldin ‘yan darikar Tijjaniya da aka shirya gudanarwa a jihar.
Daruruwan mutane ne suka soma hallara filin daga sassa daban-daban na kasar da kuma wasu kasashe makwabta,‘yansanda kuma suka hana su shiga wurin bisa dalilin barazanar tsaro.
Gwamnatin Kano ta yi watsi da sanarwar tare ta kuma tilasta jami’an janyewa da kuma gudanar da taron ranar Asabar.