Mazauna ƙauyen Auyakawa da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun dakile wani yunƙurin satar shanu, inda suka yi nasarar kwato shanu biyu da ake zargin wasu barayi sun sace.
Bayanin hakan ya fito ne cikin wani saƙo da masanin harkokin tsaro, Bakatsine, ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.
A cewar saƙon, ana zargin barayin sun sace shanun biyu ne daga gidan wani mutum mai suna Sha’aban Abdullahi da misalin ƙarfe uku na dare.
Rahoton ya ce da samun labarin faruwar lamarin, matasan ƙauyen tare da sauran mazauna yankin suka haɗa kai wajen bin sawun waɗanda ake zargin, inda suka riƙa binsu ta cikin dazuka da jeji na tsawon sa’o’i.
An ce yayin da matasan ke matsa musu, waɗanda ake zargin sun yi watsi da shanun a cikin dajin Dalanbai tare da tserewa domin gujewa kamuwa.
Bakatsine ya ce, “A daren jiya, mazauna ƙauyen Auyakawa da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun dakile yunƙurin satar shanu bayan sun bi sawun barayin na tsawon sa’o’i. Ana zargin sun sace shanu biyu daga gidan Sha’aban Abdullahi da misalin ƙarfe uku na dare, amma suka yi watsi da su a dajin Dalanbai yayin da matasan ƙauyen suka matsa kusa da su. An kwato shanun cikin nasara, sai dai waɗanda ake zargin sun tsere.”
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
