Wata kotun Amurka ta yi watsi da ƙarar ɓata suna da shugaban ƙasar Donald Trump ya shigar kan jaridar Wall Street Journal da kuma attajirin nan mai kafafen yada labarai Rupert Mardoch.
Jaridar ta wallafa rahoton cewa Mista Trump ya aike wa marigayi Jeffrey Epstein, wanda aka samu da hannu a laifukan cin zarafin yara ta hanyar lalata, wani sakon taya murnar ranar haihuwarsa mai dauke da kalamai masu nuna sha’awa, tare da hoton zanen siffar jikin mace tsirara.
Fadar White House ta musanta ingancin wasikar, tana mai cewa Mista Trump ba shi ne ya zana hoton ba, kuma bai sanya hannu a kai ba.
Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce Mista Trump bai iya gabatar da hujjar da za ta nuna cewa an wallafa rahoton ba daidai ba.
