Shugaban ƙaramar hukumar Gboko a jihar Benue, Torseer Yina, ya sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari, bayan zanga-zangar masu sana’ar achaba ta rikide zuwa tashin hankali.
Sanarwar da sakataren ƙaramar hukumar, Vincent Nev, ya fitar ranar Alhamis, ta ce dokar ta fara aiki nan take, ranar 8 ga Oktoba, 2026, domin shawo kan rikicin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Zanga-zangar ta biyo bayan kashe wani mai sana’ar achaba da wasu da ba’a san ko su waye ba suka yi a yankin Gboko ta kudu a daren laraba, an ce maharan sun harbe shi sannan suka tafi da babur ɗinsa.
Sai dai zanga-zangar da mambobin ƙungiyar masu sana’ar achaba ta Benue, BEMOA, suka gudanar ta rikide zuwa tashin hankali, inda wasu da ake zargin sun kutsa cikin zanga-zangar suka ƙona motoci biyu na hukumar Civil defense ta jihar Benue, haka kuma, an dakatar da shugabancin reshen ƙungiyar na Gboko nan take.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi gargaɗin cewa za’a ɗauki mataki kan duk wanda ya karya dokar ko ya tayar da hankalin jama’a, sai dai an ware masu gudanar da muhimman ayyuka da motocinsu daga dokar hana zirga-zirgar.
