Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe sama da Naira biliyan 1.7 wajen yaƙi da tamowa, inganta abinci mai gina jiki ga mata da yara, tare da ƙarfafa ayyukan kula da masu fama da matsalar a jihar.
Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026.
A cewar sanarwar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana tamowa a matsayin babbar barazana ga lafiyar jiki da ci gaban ɗan Adam, yana mai cewa gwamnatinsa ta tsara manufofi da shirye-shirye domin inganta abinci mai gina jiki a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 500 a matsayin gudunmawarta, da nufin jawo ƙarin tallafi daga abokan hulɗa domin faɗaɗa shirye-shiryen yaƙi da tamowa.
Gwamnatin ta ce shirye-shiryen sun taimaka wajen inganta ciyar da jarirai da ƙananan yara, samar da muhimman sinadarai masu gina jiki, da kuma kula da mutanen da ke fama da matsananciyar tamowa.
Ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa matakan da suka dace domin rage matsalar tamowa da kuma inganta lafiyar mata da yara a faɗin Jihar Katsina.
