Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta kano KAROTA, ta ɗaga darajar ma’aikatan ta sama da 300 zuwa mukamai daban-daban tare da inganta walwalarsu, da nufin ƙarfafa musu gwiwar zama jakadu nagari a ayyukan su.
Shugaban hukumar, Injiniya Faisal Mahmud Kabir ne, ya bayyana hakan yayin wani biki da hukumar ta shirya a shalkwatarta.
Injiniya Faisal ya ce a tsawon lokacin da ya shafe yana jagorantar hukumar ta KAROTA ya samar da nasarori daban-daban wajen inganta ayyukan hukumar da ma’aikanta da kuma samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar Kano.
Injiniya Faisal ya ce hukumar ta kuma karrama wasu daga cikin ma’aikatanta domin yabawa da kuma amincewa da ƙwazon da suka nuna yayin gudanar da ayyukansu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Faisal na yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar wajen gudanar da ayyukanta, tare da kira ga jami’an KAROTA da su ci gaba da aiki bisa ƙa’idoji da bin dokokin hukumar.
