Gwamnatin Kano ta gargadi ɗalibai da matasan jihar, da su guji shan miyagun ƙwayoyi, la’akari da yadda matsalar ke barazana ga rayuwar su da makomar al’umma.
Kwamshinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne yayi gargaɗin a wajen taron wayar da kan ɗalibai da matasa a wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Waiya, ya ce taron na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na ilimantar da ɗalibai maza da mata da sauran matasa kan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tare da sanya musu kishin ƙasa da shiga harkokin gina al’umma, wanda hakan ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar ƙarƙashin shirin Kano First Agenda.
Da yake jawabi, shugaban taron, Farfesa Hafiz Abubakar, ya ce haɗin kan al’umma shi ne ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin samar da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikin Kano da Najeriya baki ɗaya, inda ya ce wajibi ne kowa ya fahimci nauyin da ke kansa wajen kare zaman lafiya da kuma taimakawa wajen ci gaban Najeriya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa a yayin taron, mahalartan sa sun jaddada cewa yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi na buƙatar haɗin gwiwar iyaye, makarantu, hukumomin gwamnati, shugabannin addini da na gargajiya da kuma matasa.
