Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJihar Kano ta samu karin sabuwar tashar radio mai suna Hikima

Jihar Kano ta samu karin sabuwar tashar radio mai suna Hikima

Date:

Jihar Kano ta samu karin sabuwar tashar radio mai suna Hikima, da ta fara yada shirye-shiryenta akan mita 93.7 a zangon FM.

Tashar wadda mallakin tsohon dan takarar gwamnan Kano ce a jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada, an kaddamar da ita a Lahadin da ta gabata.

Samun karin tashar Hikima dai, ya sa adadin tashoshin radio da ake da su a nan Kano ya haura 30.

Tuni sabuwar tashar ta Hikima ta nada dan jarida Usman Usman a matsayin babban daraktanta, yayin da ta nada Abubakar Isah Dandago a matsayin babban manaja.

Tashar ta kuma dauki ma’aikata daga sauran kafafen yada labarai, ciki kuwa har da nan Premier radio.

Yanzu haka dai tashar na ci gaba da gabatar da shirye-shiryen gwaji kamar yadda mafi yawancin sabbin gidajen radio suka saba.

Da yake tsokaci kan yawaitar gidajen radio a nan Kano, shugaban sashen nazarin aikin jarida a jami’ar Bayero, Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi, ya ce yawaitar gidajen rediyo abu ne mai kyau matukar za su samar wa masu saurarensu abin da suke bukata.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...