Gwamnatin jihar Edo ta rufe wasu makarantu uku da ke yankin Edo ta Arewa sakamakon barazanar tsaro da hukumomin DSS suka bayar kan yiwuwar sace ɗalibai.
Tun da farko hukumar DSS ta bayyana cewa bayanan sirri sun nuna wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne na shirin kai hare-hare tare da sace ɗalibai a wasu sassan jihar.
Makarantun da aka rufe sun hada da Ososo Grammar School, Ososo Comprehensive High School da kuma Makeke Secondary School da ke ƙaramar hukumar Akoko-Edo.
Ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce an dakatar da dukkan harkokin karatu da gudanarwa a makarantun har sai wani lokaci.
Sai dai ɗaliban da ke rubuta jarabawar WAEC za su ci gaba da rubuta jarabawarsu karkashin tsauraran matakan tsaro tare da haɗin gwiwar al’umma.
Gwamnatin jihar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
