
Aminu Abdullahi Ibrahim
Al’ummar kasuwar Kofar Wambai sun zargi gwamnatin Kano da yinkurin sayar da tashar motar kasuwar.
’Yan kasuwar sun yi wannan koke ne yayinda suke ganawa da manema labarai a Litinin din nan.
Da yake jawabi shugaban kungiyar direbobi na tashar Kofar Wambai, Ibrahim Idris Shugaba, ya ce sun shafe fiye da shekaru 28 suna gudanar da kasuwanci da tuki a kasuwar amma kwatsam yanzu gwamnati ke shirin kwace musu.
Ya ce suna rokon gwamna Abba Kabir Yusuf ya dakatar da shirin sayar da gurin duba da yawan mutanen da zasu rasa aikin yi.
A nasa bangaren shugaban kungiyar masu sayar da Jinns da T-shirt na kasuwa, Musbahu Ibrahim Sudawa, ya ce ba wannan ne karon farko da gwamnati ke yanka tashar ba.
Ya ce a yanzu idan aka sake yanka tashar ba za a samu gurin da motoci zasu rinka sauke kaya ba.
Musbahu Sudawa, ya roki gwamnatin Kano ta gaggauta dakatar da yinkurin sake gine tashar la’akari da matasan da zasu rasa guraren kasuwancinsu.
