Shugaban rundunar sojin ƙasa na Kasar nan, Janar Waidi Shuaibu ya bada umarnin tura ƙarin sojoji 850 Jihar Filato domin tabbatar da tsaro sakamakon tashin hankalin da ya yi sanadiyar asarar rayuka a jihar.
Mai magana da yawun rundunar sojin dake aikin samar da zaman lafiya a jihar, Kaftin Chinonso Polycarp Oteh ne ya sanar da matakin, a dai dai lokacin da hukumomi ke lalubo hanyar dawo da zaman lafiya a garin Jos, bayan ƙazamin harin da ya laƙume rayukan mutane a ranar lahadin da ta gabata.
Oteh ya ce ana saran tura ƙarin sojojin ya taimaka wa waɗanda ke aiki a jihar wajen kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a a fadin jihar baki ɗaya.
Shugaban ya tabbatar wa dakarun cewar an tanadar musu da isassun kayan aiki da kuma haƙƙoƙin su domin ganin sun samu nasarar da ta kamata.
Kakakin rundunar sojin ya ce an ɗebo sojojin 850 daga Abuja da Kaduna domin taimakawa na Filato gudanar da aikin samar da tsaron.
