Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari makarantar sakandiren gwamnati da ke Iluke Bunu a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi, inda suka kashe mutane uku ciki har da mataimakin shugaban makaranta, tare da sace wasu ɗalibai.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:45 na safiyar ranar Laraba, yayin da ɗalibai ke rubuta jarabawar WAEC.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne kan cibiyar jarabawar da ɗalibai daga al’ummomi uku ke rubuta jarabawar kammala sakandire ta WASSCE.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandiren gwamnati ta Aharha-Bunu, Malam Gani Anifowose, tare da wasu mutum biyu.
Rahotanni sun kuma ce an sace ɗalibai uku da wasu mazauna yankin yayin harin.
Shugaban ƙaramar hukumar Kabba-Bunu, Honarabul Zacchaeus Dare Michael, ya yi tir da harin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da rashin tausayi.
Ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da tabbatar da cewa ana ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata laifin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da harin, inda ta ce maharan dauke da makamai sun shiga yankin ne a kan babura kusan arba’in da nufin sace ɗalibai da mazauna yankin.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, sojoji da masu sintiri sun yi artabu da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji.
Sai dai rundunar ta ce har yanzu babu cikakkiyar shaida da ke nuna cewa an yi garkuwa da ɗalibai masu yawa kamar yadda ake yadawa.
Ta kuma bayyana cewa an kashe ɗaya daga cikin maharan yayin musayar wuta, yayin da wani jami’in tsaro ya samu raunin harbin bindiga kuma yake karɓar magani.
Jami’an tsaro na ci gaba da farautar maharan domin hana sake kai hare-hare a yankin.
