Ishaq Sani Dambazau
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 10 ga watan Yuni a matsayin ranar da za’a riƙa tunawa da muhimmancin tattaunawa tsakanin al’umma mabanbanta domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin duniya.
A Najeriya, ƙasa mai ɗauke da ƙabilu da addinai mabambanta, masana na ganin akwai buƙatar ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’umma domin tabbatar da haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.
Yaya zamantakewar ku ke kasancewa da wasu kabilun yayin da ake bikin ranar muhimmancin tattaunawa tsakanin al’umma mabanbanta?
