Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya soki jam’iyyar NDC bisa kasa tsayar da ɗan takara a zaɓen cike gurbin Dan Majalisar tarayya na Dawakin Kudu da Warawa, inda ya bayyana hakan a matsayin gazawa a bayyane, da tabbatar da cewa jam’iyyar bata da manufa ko tushe a tsakanin al’umma.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamnan ya bayyana sakamakon zaɓen a matsayin wata alama da ke nuna irin nasarar da jam’iyyar APC ke sa ran samu a babban zaɓen shekarar 2027, la’akari da yawan fitowar jama’a domin kaɗa ƙuri’a tare da gudanar da zaɓen cikin lumana.
Gwamna Abba ya ce an gudanar da zaɓen cikin adalci, gaskiya da sahihanci, lamarin da ya nuna ra’ayin masu zaɓe ba tare da wata tangarda ba, tare da yabawa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, bisa nasarar gudanar da zaɓen, tare da jinjinawa jami’an tsaro kan tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito
Gwamna Yusuf na cewa yadda aka gudanar da zaɓen da sakamakonsa sun ƙara tabbatar da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya, tare da taya ɗan takarar APC murnar samun nasara, da yin kira gare shi da ya mayar da hankali wajen wakiltar al’umma yadda ya kamata domin cika burinsu.
