Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa gwaje-gwajen da aka yi wa wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, sun nuna cewa ba sa ɗauke da cutar.
Darakta-Janar na hukumar, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce an gudanar da gwaje-gwajen sau biyu, kuma dukkan sakamakon ya nuna cewa mutanen ba su kamu da Ebola ba.
A cewarsa, an kai rahoton mutanen biyu ga cibiyar kula da ayyukan gaggawa na lafiyar jama’a ta Jihar Adamawa a ranar 30 ga Oktoba, bayan sun nuna wasu alamomin rashin lafiya da suka sa aka yi zargin kamuwa da cutar.
Dakta Idris ya ce an killace mutanen tare da ɗaukar samfurin jininsu domin gudanar da gwaje-gwaje, yayin da aka aiwatar da matakan kariya daga yiwuwar yaɗuwar cutar.
Ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu wani mutum da aka tabbatar yana ɗauke da cutar Ebola a Jihar Adamawa.
Shugaban NCDC ya ƙara da cewa hukumar na ci gaba da haɗa kai da gwamnatin Adamawa da Ma’aikatar Lafiyar jihar domin ƙarfafa matakan kariya da sa ido kan cututtuka masu yaɗuwa.
