Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta bari fasahar Ɗan Adam ta Ƙirƙira (AI) ta zama sanadin ƙayyade wanda zai lashe zaɓen 2027 ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙasa da ƙasa kan AI da dimokuraɗiyya da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyar Yiaga Africa ta shirya tare da haɗin gwiwar INEC da sauran abokan hulɗa.
Amupitan ya jaddada cewa ikon zaɓen wanda zai jagoranci Najeriya yana hannun al’ummar ƙasar, ba na na’urori ko wasu tsare-tsaren kwamfuta ba.
Sai dai ya bayyana cewa AI na iya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin zaɓe, musamman wajen jigilar kayan zaɓe, nazarin bayanan sakamako, gano kura-kurai da kuma ƙarfafa tsaron tsarin zaɓe.
Ya ce INEC ta riga ta kafa sashen kula da fasahar AI a cikin sashen fasahar sadarwa na hukumar, tare da kammala tsarin dokokin amfani da fasahar a harkokin zaɓe.
Shugaban INEC ya kuma yi gargaɗin cewa duk da amfanin fasahar, akwai haɗarin amfani da ita wajen yaɗa bayanan ƙarya da kai hare-hare kan tsarin zaɓe.
A nasa jawabin, Daraktan ƙungiyar Yiaga Africa, Samson Itodo, ya ce babban ƙalubalen da ke gaban zaɓen 2027 shi ne dawo da amincewar ’yan Najeriya kan sahihancin tsarin zaɓe.
