Saurari premier Radio
43.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIna da yakinin al'ummar Kano APC za su zaba-Ganduje

Ina da yakinin al’ummar Kano APC za su zaba-Ganduje

Date:

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce al’ummar Kano za su zaɓi APC a 2023 kamar yadda suka saba.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Asabar lokacin da yake jawabi a wajen buɗe ofishin yaƙin neman zaɓen gwamna da na shugaban ƙasa na APC.

“Kano ce APC kuma APC ce Kano. Saboda haka al’ummarmu a shirye suke kuma muna neman goyon bayansu”, in ji Gwamna Ganduje.

A jawabinsa, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce jam’iyyar za ta yi nasara a dukkan zaɓuka a 2023.

“Abin da na gani ta fuskar shirye-shirye da tsare-tsare a ofishin kamfe ɗin nan ya birge ni”, in ji shi.

Mista Tinubu ya ce ba kamfe ne ya kawo shi Kano ba, ya zo ne kawai don ƙaddamar da ofishin da kuma duba yadda yake.

Ya ce idan aka zaɓe shi, zai tabbatar ya ɗora ƙasar nan akan gwadabe mai kyau, kuma ‘yan Najeriya ba za su yi nadamar zaɓen sa ba.

“Za mu yi amfani da tsintsiyarmu don tsaftace ƙasar nan tare da ba dukkan ‘yan Najeriya farin ciki”, in ji Tinubu.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories