Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, inda ta jaddada ƙudurinta na tsaftace tsarin jarabawa da kuma harkokin shigar da ɗalibai manyan makarantu.
JAMB ta ce matakin korar ma’aikacin na nuna cewa manufarta ba rashin sassauci kan cin hanci da rashawa da kuma rashin ɗa’a ta shafi dukkan ma’aikata, ba tare da la’akari da matsayinsu ba.
Hukumar ta kuma gargadi ma’aikatanta da kada su yi amfani da mukamansu wajen cin zarafin masu jarabawa ko amfanin kansu, tana mai cewa ba za ta kare duk wani ma’aikaci da ya ci amanar jama’a ba.
JAMB ta ƙara tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan ladabtarwa kan ma’aikatan da suka aikata ba daidai ba, domin kare mutuncin tsarin jarabawa da kuma amincewar jama’a ga ayyukan hukumar.
