
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya kafa wani kwamiti na musamman, kan shirye-shiryen daukar matakan kariya daga cutar Ebola, tare da amincewa da sakin naira biliyan 10 domin aiyukan gaggawa don dakile yaduwar cutar.
Mai bawa shugaban kasa Shawara kan harkokin yada labarai da dabarun aiki Bayo Onanuga, ya ce shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne zai kasance shugaban kwamitin, wanda kuma ya kunshi wakilan ma’aikatu da hukumomi da kuma jihohi.
Hakan na zuwa ne biyo bayan yadda annobar Ebola ke ci gaba da bazuwa a ƙasashen Dimokuraɗiyyar Kongo da Uganda, inda zuwa yanzu rahotanni suka tabbatar da cutar ta kashe aƙalla mutane 349, yayinda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ayyana lamarin a matsayin matakan gaggawa kan lafiyar alummar duniya.
Tinubu ya umarci a ƙara tsaurara binciken fasinjoji a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, musamman masu zuwa daga yankunan da cutar ta fi kamari.
Haka kuma ya ba da umarnin buɗe cibiyoyin killace wadanda ake zargin kamuwa da cutar a filayen jiragen sama na Legas da Abuja.
Masana sun ce har yanzu babu ingantaccen rigakafi ko magani da aka amince da shi domin wannan cuta, sai dai kulawar gaggawa na iya taimakawa wajen ceton rayuka.
