Hukumar NAHCON, ta sanar da kuɗin aikin Hajjin 2027 da maniyyatan Najeriya za su biya.
Farashin ya bambanta gwargwadon yankin da za a tashi zuwa Saudiyya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce gwamnatin tarayya ta amince da kuɗaɗen ne bayan tattaunawa da shugabannin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kuma masu ruwa da tsaki a Saudiyya.
NAHCON ta kuma sanya ranar 26 ga Satumba 2026 a matsayin ranar ƙarshe kuma ta kammala ɗora bayanan na dukkan maniyyatan Hajjin 2027.
Za a ɗora bayanan ne a tsarin intanet na Nusuk-Masar.
Hukumar ta ce ba za a ƙara wa’adin ba.
NAHCON ta ce dole ne jihohi su kammala tura dukkan kuɗaɗen aikin Hajjin 2027 zuwa 2 ga Disamba 2026.
NAHCON ta yi gargadin cewa rashin cika wa’adin da aka sanya na iya kai wa ga rasa kujerun Hajjin da aka ware wa jihar.
