Gwamnatin Kano ta ce za ta kafa ƙarin sansanonin sojoji tare da tura jami’an tsaro dazuzzuka a ƙananan hukumomin da ke fuskantar matsalolin tsaro a jihar, domin ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Kwamishinan Ƙananan hukumomi da harkokin masarautu Muhammad Tajo Othman ne, ya bayyana hakan bayan wani taro tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Tajo Othman ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawar gwamnan da Ministan Tsaro na Najeriya, inda sabbin matakan tsaron za su ƙarfafa tsarin da jami’an ’yan sanda da na tsaron unguwanni ke gudanarwa, musamman wajen saurin kai ɗauki yayin fuskantar barazanar tsaro.
Tajo ya ce gwamnatin ta kuma amince da kafa cibiyoyin gwajin kwamfuta da fasahar sadarwa a kowace ƙaramar hukuma, inda tuni aka bayar da kwangilolin aikin, da nufin taimakawa ƙoƙarin jami’an tsaro da al’ummar yankin dabarun gano marasa gaskiya domin daukar matakin gaggawa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamnatin da shugabannin ƙananan hukumomin sun kuma umarci hukumomin da abin ya shafa da su fara aiwatar da dukkan shawarwari da matakan da aka cimma a taron cikin gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaron da ke kokarin kunna kai a jihar Kano.
