Gwamnatin Kano ta ce tana sa ran fara faɗaɗa rarraba ruwan sha ga al’ummomi a faɗin jihar cikin mako guda, yayin da take dab da kammala aikin farfaɗo da manyan cibiyoyin sarrafa ruwa, rijiyoyin ajiya da tsare-tsaren samar da ruwa na yankuna.
Kwamishinan albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi na Dr Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana hakan, inda ya ce manyan cibiyoyin samar da ruwan da suka hada da masana’antar sarrafa ruwa ta Challawa, Tamburawa da rumbun ajiyar ruwa na Goron Dutse, na dab da komawa aiki yadda ya kamata.
Dr Dahiru ya ce an gyara wasu manyan layukan isar da ruwa, ciki har da layin da ya kai tsawon kilomita 15.6 zuwa Goron Dutse, tare da kwashe laka da gyara rijiyoyin ajiya masu ɗaukar sama da lita miliyan 40.
Kwamshinan ya ce yanzu haka angama gyara famfunan ruwa da na’urorin tace ruwa, yayin da tsare-tsaren ruwan yankuna tara daga cikin 19 na jihar ke kan aikin farfaɗowa, inda wasu tuni suka fara samar da ruwa bayan shafe shekaru ba sa aiki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na cewa aikin gyaran ruwan na daga cikin dabarun gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na rage gibin ruwan da ake fuskanta a birnin Kano, wanda ake bukatar fiye da lita miliyan 300 a kowace rana.
