Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin yin nazari kan tsarin samar da magunguna da kayan aikin lafiya, wanda zai dinga gudana duk bayan wata uku domin ƙarfafa haɗin gwiwa, inganta aiki da kuma tabbatar da wadatar magunguna a cibiyoyin lafiya na gwamnati.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin taron nazarin ayyukan watanni shidan farkon 2026 da muke ciki na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Amfanin Lafiya na Kano, wato DMCSA.
Ya kuma ce daga yanzu taron ba zai tsaya kan ayyukan Hukumar kaɗai ba, za’a haɗa dukkan shirye-shiryen da masu ruwa da tsaki dake gudanar da ayyukan samar da magunguna a ɓangaren lafiya, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta yanke shawara.
Tun da farko, Daraktan hukumar Pharmacist Gali Sule, ya buƙaci amincewar Kwamishinan Lafiyar domin faɗaɗa taron bayan nasarorin da aka samu tun bayan fara gudanar da shi, inda ya ce taron na ba da damar tantance nasarori da ƙalubalen da aka fuskanta cikin watanni uku tare da tsara matakan inganta ayyuka a zangon da zai biyo baya.
