Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon motoci 78 ga rundunar yansandan Kano domin bunkasa harkokin tsaro a kananan hukumomi 44 na jihar.
Da yake jawabi a Talatar nan, Abba Kabir Yusuf ya ce za a raba motocin ne ga ofisoshin yansanda 78 da ke kananan hukumomin jihar Kano.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma, su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai da kuma bayanan inda ake aikata laifuffuka domin magance su.