Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta sauke wasu shugabannin cibiyoyin kiwon lafiya a karamar hukumar Gezawa daga muƙamansu, tare da dakatar da albashin wasu ma’aikatan saboda samun su da laifin rashin zuwa wajen aiki akan lokaci.
Matakin ya biyo bayan wata ziyarar bazata da Shugaban Hukumar, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya kai zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na Tsalle da Gofaro dake Gezawan domin tantance yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya.
Da yake yiwa Premier radio karin bayani, Farfesa Salisu ya ce, tuni hukumar sa ta maye gurbin dakatattun shugabannin cibiyoyin kiwon lafiyar na Tsalle da Gofaro da Mataimakan su har sai an kammala bincike, tare da yin gargaɗin cewa gwamnati ba za ta ƙara lamuntar sakaci ko rashin zuwa aiki ba.
Sai dai a cibiyar kiwon lafiya ta Panshekara da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Farfesa Salisu ya jinjinawa ƙwazon ma’aikata da haɗin kan al’umma bayan da ya gano cewa an samar da na’urar duba cikin mata masu juna biyu domin inganta kula da lafiyar iyaye mata da jarirai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Farfesa Salisu na jaddada cewa Hukumar kula da lafiya ta matakin farkon za ta ci gaba da hukunta masu sakaci tare da karrama ma’aikata da cibiyoyin da suka nuna ƙwazo, domin tabbatar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya a faɗin Kano.
