Gwamnatin Kano ta ce binciken ta ya gano cewa, ƙananan asibitocin dake yankunan karkara, suna bukatar ma’aikatan lafiya kimanin 3,900 domin gudanar da ayyukan su yadda kamata.
Kwamshinan lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ganawa da Premier Radio.
Dr Labaran ya ce tuni gwamnati ta umarci hukumar kula da lafiya a matakin farko da ƙananan hukumomi 44 na jihar umarnin ɗaukar adadin ma’aikatan domin cike giɓin da ake da shi, kasancewar matsalolin kula da lafiya sun fi ta’azzara ne a kauyuka.
Dr Abubakar Labaran ya ce a baya-bayan nan da gwamnati ta buɗe damar ɗaukar ma’aikatan lafiya, fiye da ƙwararrun ma’aikatan lafiya dubu 22 ne suka nemi aikin, sai dai gurbin mutane 2,037 kawai gwamnati take da shi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Labaran na cewa tuni ma’aikatar sa ta nemi izinin sake ɗaukar wasu ma’aikatan lafiyar 1,600 a kashi na biyu domin ƙara inganta ɓangaren kiwon lafiya a faɗin Kano.
