Gwamnatin Kano ta ce limaman masallatai na da gagarumar rawar takawa musamman a hudubobin su na sallar juma’a wajen wayar da kan al’umma kan muhimmanci da fa’idar shirin auren gata da gwamnatin jihar ta gudanar.
Kwamishinan yaɗa labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakuncin mambobin kungiyar Matasan limaman masallatan juma’a suka kai masa ziyara.
Kwamishinan ya nuna damuwa kan yadda wasu marasa kishin Kano suke yada hotunan wasu dattawa a kafafen sada zumunta, suna ikirarin cewa suna daga cikin mutanen da aka aurar a karkashin shirin auren gata, inda Waiya ya ce dattawan da ake yadawa tsofaffin jami’an hukumar Hisbah ne, wanda kuma kasancewarsu a wajen taron bai kamata a fassara shi da cewa suna daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin auren gatan ba.
Da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar, Imam Gwani Sani Tilo, ya yaba da ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman shirye-shiryen da suka shafi harkokin addinin Musulunci da jin dadin al’ummar jihar Kano, inda ya ce ƙungiyar ta su zata yi dukkan abinda ya dace wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin shirin na auren gata da sauran tsarukan da zasu ciyar da al’umma gaba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwamared Waiya na
jaddada muhimmiyar rawar da limamai da malaman addinin Musulunci ke takawa wajen ilmantar da al’umma, karfafa zaman lafiya da fahimtar juna, da kuma dakile yada bayanan karya da ka iya haifar da rashin fahimta a tsakanin al’umma.
