Gwamnatin Kano ta ce tana ƙara zurfafa haɗin gwiwa da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta ayyukan kiwon lafiya da kyautata alaƙar gwamnati da al’ummar jihar.
Shugaban hukumar samar da Magunguna da kayan aikin lafiya na Kano Pharmacist Gali Sule ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar limaman ƙadiriyya reshen Kano.
Ghali Sule ya ce shugabannin addinai na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a, bunƙasa zaman lafiya, yana mai cewa gudummawar da suke bayarwa na taimakawa wajen aiwatar da manufofin gwamnati da haɓaka harkokin kiwon lafiya.
A jawabinsa tunda farko, Shugaban majalisar limaman ƙadiriyya reshen Kano, Sheikh Hassan Mukhtar Atamma, ya ce sun kai ziyarar ne domin gabatar da shugabannin majalisar tare da shimfiɗa kyakkyawar alaƙar aiki da Hukumar, inda ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da ke inganta lafiyar al’umma, zaman lafiya da ci gaban Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Ghali Sule na cewa hukumar a shirye take wajen ci gaba da yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ingantaccen tsarin samar da magunguna da ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar Kano.
