Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Jihar Zamfara Ta Rufe Kasuwannin Shanu Guda 11 Saboda Matsalar Yan...

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Rufe Kasuwannin Shanu Guda 11 Saboda Matsalar Yan Bindiga

Date:

Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin rufe kasuwannin sayar da shanu guda 11 a sassa daban-daban na jihar har sai baba-ta-gani.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Munnir Haidara ne ya fitar da sanarwar a Larabar nan, inda ya ce, an yanke shawarar rufe su ne sakamakon rahotannin tsaro da ke nuni da cewa, yan fashin daji na amfani da wadannan kasuwanni wajen sayar da shanunsu da suka sato.

Kasuwannin da umurnin ya shafa sun hada da ta Tsafe da Bilbis a karamar hukumar Tsafe da kasuwar Jangebe a karamar hukumar Talata-Mafara da kasuwar Wuya a karamar hukumar Anka.

Umurnin ya kuma hada da kasuwar Magamin Diddi da ke karamar hukumar Maradun da kasuwar Galadi a karamar hukumar Shinkafi, da kasuwar Mada a karamar hukumar Gusau, da Sabon Birnin Dan-Aii a karamar hukumar Birnin Magaji.

Sai kuma kasuwannin Kokiya da Chigama da Nasarawar Godel, da ke cikin karamar hukumar Birnin Magaji.

Gwamnati ta umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin umarnin doka, in da ta bukaci al’ummar jihar da su bi wannan umarni tare da hada kai da gwamnati a kokarin kawar da ayyukan yan ta’adda.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...