Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo tare da kama wadanda suka kashe fitaccen me sharhi akan siyasa a kafafen sada zumunta Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu.
Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin abin firgitarwa da kuma abin da ba za’a amince da shi ba, yana mai cewa lamarin na bukatar cikakken bincike domin gano musabbabin kisan tare da gurfanar da duk wadanda suke da hannu a gaban kotu.
Gwamna Yusuf ya baiwa rundunar ‘yan sandan Kano da hukumar DSS umarnin kara kaimi wajen gano wadanda suka aikata kisan tare da tabbatar da ganin an hukunta su.
Gwamnan ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da abokansa da kuma abokan huldarsa, yana addu’ar Allah Ya gafarta masa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na yin kira ga al’ummar Kano da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannu, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
