Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gargadi sababbin ma’aikatan lafiya 2,037 da gwamnatin sa ta dauka, da su guji wulaƙanta marasa lafiya ko karɓar kuɗi a hannun su kafin ganin likita, ko samun kulawar gaggawa a duk asibitocin jihar.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne lokacin da yake miƙa takardun ɗaukar aiki ga sabbin ma’aikatan lafiyar su 2,037, da nufin rage ƙarancin ma’aikata da ake fuskanta a cibiyoyin lafiya a faɗin Kano.
Gwamnan Abba ya ce daga cikin sabbin ma’aikatan da aka ɗauka akwai ƙwararrun likitoci 250, masu harhada magunguna 40, ma’aikatan jinya 250, ungozoma 250, manyan malaman kula da lafiya a matakin farko 150, ƙananan ma’aikatan kula da lafiya 50 da masu binciken cututtuka 50, da wasu sauran ƙwararrun.
Gwamnan ya ce ɗaukar ma’aikatan ya zama dole sakamakon ƙarancin ma’aikatan lafiya da kano ke fuskanta, wanda hakan ya ƙara tsananta ne sakamakon fita da likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya ke yi zuwa wasu wuraren.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na buƙatar sabbin ma’aikatan da su gudanar da aikinsu cikin tausayi, gaskiya, ladabi da ƙwarewa, tare da mutunta haƙƙi da darajar dukkan marasa lafiya ba tare da la’akari da matsayinsu, addini, ƙabila ko ra’ayinsu na siyasa ba.
