Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa dakatar da shirin ƙarin kuɗin jarrabawar NECO da gwamnatin sa tayi, wanda gwamnan ya ce hakan zai bunƙasa fannin ilimi a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rabon takardun aikin gwamnati ga sabbin malamai 4,900 da kuma Malaman BESDA 3,688 na shirin ABBA Gida-Gida, wanda ya gudana a rufaffen ɗakin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Gwamna Abba ya ce ware kashi 31 cikin 100 na kasafin kuɗin shekarar 2026 ga fannin ilimi da gwamnatin sa ta yi, ya taimaka wajen ganin Kano ta zama ta farko a sakamakon jarabawar NECO na bana.
Gwamnan ya kuma gargadi sabbin malaman da su kasance masu bin ƙa’idojin aikin gwamnati da nuna ƙwarewa da kishin Kano da al’ummar da suke rayuwa a cikin su domin samar nagartattun ɗalibai da Kano da duniya zata yi alfahari da su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, Ministan Ilimi na ƙasa, Dr Ma’aruf Tunji Alausa, na yabawa gwamnatin Kano bisa ƙoƙarin da ta nuna wajen zuba jari a ɓangaren ilimi, yayin da Kwamishinan Ilimi, Gwani Ali Haruna Makoda, da Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta Kano SUBEB, Malam Kabir Yusuf Kabir, suka jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen bunƙasa ilimi.
