Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da zasu bunƙasa ɓangaren ilimi ta hanyar ƙarfafa shirin haɗin gwiwar inganta fannin wanda ƙasar Birtaniya ke tallafawa jihar fiye da shekaru biyar da suka gabata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr Ali Abubakar Haruna Makoda, yayin taron miƙa ragamar shirin da aka gudanar a Kano.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa tsare-tsaren ilimi, bunƙasa ƙwarewar malamai, samar da ingantattun kayan koyo da koyarwa, tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar yin karatu mai inganci.
Ya kuma yabawa Gwamnatin Birtaniya bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta ilimi a Kano, inda ya ce shirin ya taimaka wajen tattara sahihan bayanai kan yaran da ba sa zuwa makaranta, da ƙarfafa koyar da karatu a matakin farko ta hanyar horas da malamai da samar da kayan koyarwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa taron ya samu halartar wakilan Hukumar Jakadancin Birtaniya, UNICEF, ƙungiyoyin ci gaba, ƙungiyoyin farar hula da manyan jami’an gwamnati, inda suka amince da matakan tabbatar da dorewar nasarorin da shirin ya samar.
