Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da Kwamitin da zai tsara sabon kundin manufofin yaƙin neman zaɓensa na shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Kwamitin dai an dora masa alhakin duba yadda aka aiwatar da kundin manufofin zaɓen shekarar 2023 mai taken “Alƙawarina ga Kano”, tare da tsara sabon kundin da zai jagoranci manufofin gwamnati idan aka sake zaɓensa a wa’adi na biyu.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba da Mataimakinsa Murtala Sule Garo, ne za su sanya ido kan aikin kwamitin, yayin da aka naɗa Dr Aminu Magashi Garba a matsayin shugaba, sai Dr Yusuf Ya’u Gambo a matsayin sakatare.
Sanarwar ta ce kwamitin ya ƙunshi jami’an gwamnati, masana da ƙwararru daga fannoni daban-daban, waɗanda aka ɗorawa alhakin tantance nasarorin da aka samu wajen aiwatar da alkawuran zaɓen 2023, gano abubuwan da ba’a kammala ba, da kuma haɗa su cikin sabon kundin manufofi na shekarar 2027.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa kwamitin zai kuma tattauna da masu ruwa da tsaki daga gwamnati da masu zaman kansu domin tattara shawarwari da sabbin dabarun da za su taimaka wajen samar da cikakken kundin manufofi mai mayar da hankali kan bukatun al’umma, tare da ƙarfafa ci gaban Kano daga shekarar 2027 zuwa 2031.
