Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta kwamitin haɗin gwiwar hukumomi masu yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da sabbin kayan aiki na miliyoyin naira.
Gwamnan ya ƙaddamar da rundunar ne ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce matakin zai taimaka wajen hanzarta ɗaukar mataki kan sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da ayyukan daba a jihar.
Abba Kabir Yusuf ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen gyaran hali da koyar da sana’o’i ga waɗanda aka rehabilitarsu daga shaye-shaye, domin ba su damar komawa cikin al’umma.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce sabuwar rundunar da kayan aikin da aka samar za su ƙarfafa yaƙi da miyagun ƙwayoyi a faɗin Kano.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su haɗa kai da hukumomin tsaro domin rage matsalar shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi.
