Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Monday, September 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamna Abba Kabir Ya Mika Wa Majalisa Sunan Farfesa Sani Lawan Malumfashi...

Gwamna Abba Kabir Ya Mika Wa Majalisa Sunan Farfesa Sani Lawan Malumfashi Domin Nada Shi Shugaban Hukumar Zabe Ta Jihar Kano

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amincewa gwamna Abba Kabir Yusuf nada karin masu bashi shawara 10.

Wannan ya biyo bayan wasikar da gwamnan ya aike gaban majlisar dokokin a Talatar nan karkashin Kakakinta Jibril Isma’il Falgore.

Bayan karanta takardar ne kuma yan majalisar suka amince da wannan bukata.

Shugaban masu rinjaye wakilin Dala, Lawan Hussini ya ce a doka dole me gwamna ya mikowa majalisa sunayen wadanda yake son madawa a matsayin masu bashi shawara.

Ya kara da cewa gwamna Abba Kabir Yusif, ya kuma nemi majalisar ta amince masa nada Farfesa Sani Lawan Malumfashi a matsayin shugaban hukumar zabe ta jihar Kano KANSEIC.

Wakilinmu, Aminu Abdullahi Ibrahim, ya ruwaito Majalisar ta bukaci Farfesa Sani Lawal Malumfashi da mutane uku da za a nada a matsayin kwamishinonin hukumar su bayyana a gabanta domin tantance su a gobe Laraba.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...