Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKylian Mbappe ya tsallake gwajin lafiyarsa a matsayin dan wasan Real Madrid.

Kylian Mbappe ya tsallake gwajin lafiyarsa a matsayin dan wasan Real Madrid.

Date:

Gaba kadan a wannan rana, za a gabatar da dan wasa Klyin Mbappe a matsayin sabon dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid daga PSG ta kasar Faransa.

Madrid ta sanar da yau Talata ne, domin gabatar da Kyaftin din kasar Faransa wanda ya Jagoranci kasar a gasar Euro 2024 da aka kammala a kasar Jamus.

Katafaren filin wasa na Santiago Bernabeu dake birnin Madrid, ne dai zai karbi bakuncin gabatar da dan wasan da kawo yanzu haka tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa a duniyar kwallon kafa.

Ana saran, tsaffin yan wasan Madrid, za su halarci bikin gabatar da sabon dan wasan da a yanzu ke sawun wanda zasu iya lashe kyautar gwarzan dan wasan duniya na bana.

Mbappe a shekarar 2018, ya jagoranci kasar sa ta Faransa lashe gasar cin kofin Duniya, zai zama dan wasa na farko da Madrid ta dauka gabbanin fara kakar wasanni ta badi.

Kawo yanzu haka, tikitin shiga filin wasa na Santiago Bernabeu tuni ya kare, gabbanin a gudanar da bikin gabatar da Kylian Mbappe.

A baya ya bugawa PSG wasanni da dama, kafin ya yanke shawarar barin kasar Faransa zuwa Sifaniya, bayan kwantaraginsa ya kare da kungiyar da ke birni Fari.

Tuni ma sabon dan wasan na Real Madrid zai sanya riga mai lamba Tara, wadda Karim Benzema ya yi amfani da ita kafin ya bar Madrid zuwa kasar Saudia Arabia.

Ahmad Hamisu Gwale

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...