24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje zai yiwa gadar Kofar Ruwa kwalliyar Milyan 500

Ganduje zai yiwa gadar Kofar Ruwa kwalliyar Milyan 500

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince  a kasha N525,435,750 wajen kawata gadar kasa ta Tijjani Hashima da ke Kofar Ruwa.

Kwamishinan yada labarai na jiha Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai, kan abinda aka tattauna a zaman majalisar ranar Alhamis.

Kwamishinan ya ce manufar fitar da kudin shi ne don a magance danshin da ake samu a gadar, a kuma mayar da ita ta zamani, tare da yi mata kwalliya da za ta da da ce da zamani.

Ya kuma ce majalisar ta amince da kasha wasu kudin N65,709,198 wajen kawata gadar kasa ta sabon titin Panshekara

Haka kuma ya ce an bayar da wata kwangilar ta gina titin kwanar gogori mai tsahon kili mita 3 da rabi a garin gogoro da ke karamar hukumar Bagwai, akan kudi N290, 265, 511.33

Latest stories