Tsohon Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahotannin da ke cewa ya zargi gwamnatin Jihar Kano da almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a ta hanyar biyan kuɗaɗe ga tsoffin kansiloli.
Cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa, Kwamared Muhammad Garba, ya fitar, Ganduje ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, kuma marar tushe, yana mai jaddada cewa bai taɓa yin wata hira da ya furta irin kalaman ba.
A cewar sanarwar, babu wani lokaci da tsohon gwamnan ya yi kalaman da aka danganta masa, tana mai zargin cewa an ƙirƙiri rahoton ne da gangan domin muzanta shi da kuma haifar da rikicin siyasa.
Snarawar ta ce, Ganduje a matsayinsa na dattijo kuma jigo a siyasa, yana da damar isar da ra’ayinsa ga jami’an gwamnati a matakin tarayya da na jiha ta hanyoyin da suka dace.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano asalin rahoton, tare da gargaɗin ɗaukar matakin shari’a akan duk waɗanda aka gano suna da hannu wajen yaɗa shi.
