Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya karɓi lambar yabon Gwamnan Shekara wadda jaridar BusinessDay ta ba shi, bisa gudunmawar da gwamnatinsa ta bayar wajen inganta shugabanci, bunƙasa tattalin arziki da samar da yanayin da ke jawo masu zuba jari a jihar.
An dai bayar da lambar yabon ne a yayin taron shekara-shekara karo na 14 na manyan shugabannin kamfanoni da jaridar BusinessDay ta shirya a otal ɗin Eko da ke Legas.
Mawallafi kuma babban jami’in gudanarwa na jaridar, Frank Aigbogun, ya ce an zaɓi Gwamna Abba ne saboda irin ci gaban da Kano ta samu wajen inganta yanayin kasuwanci da jawo masu zuba jari.
A saƙonsa na godiya, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, ya bayyana cewa karramawar ta samo asali ne daga ƙoƙarin gwamnatinsa na aiwatar da shugabanci mai anfani ga al’umma da sauye-sauyen da suka taimaka wajen bunƙasa ci gaban jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su ƙarfafa kasuwanci, tallafawa ƙanana da matsakaitan masana’antu, bunƙasa noma, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma aiwatar da ƙarin ayyukan raya ƙasa domin inganta rayuwar al’ummar Kano.
