Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila ta karrama fitaccen malamin addinin Musulunci kuma shugaban majalisar malamai ta Kano Sheikh Ibrahim Khalil, da digirin girmamawa, saboda gudunmawar da ya dade yana bayarwa wajen ci gaban ilimi, addini da al’umma.
An karrama Sheikh Khalil ne yayin bikin yaye dalibai na jami’ar rukuni na biyu da na uku, su dubu daya da dari daya da daya, a wani taro da ya gudana a harabar jami’ar da ke garin Sumaila.
Jami’ar ta bayyana Sheikh Ibrahim Khalil a matsayin daya daga cikin fitattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma, musamman ta fannin ilimantarwa, wa’azi da kuma ayyukan da suka shafi ci gaban addini da rayuwar jama’a.
Bikin ya samu halartar manyan baki, malamai, wakilan hukumomi da kungiyoyi daban-daban, yayin da daliban da suka kammala karatunsu a fannoni daban-daban suka karbi shaidun kammala karatu.
A yayin bikin yaye ɗaliban, Shugaban jami’ar Farfesa Abdulhadi Sale Kumurya ya bukaci daliban da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen amfanar da al’umma, tare da bayar da gudunmawa wajen gina al’umma mai ilimi da kyakkyawar makoma.
