Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya cire jami’an da ba su da ƙwarewa daga cikin gwamnatinsa, yana mai cewa kasancewarsu na janyo mata suka da abin kunya.
Ndume, wanda tsohon Shugaban Marasa Rinjaye ne a Majalisar Dattawa kuma jigo a jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV.
Sanatan ya yi amfani da kalmar “kakistrocrats” wajen bayyana mutanen da, a cewarsa, ba su da ƙwarewa ko cancantar gudanar da mulki. Ya ce irin waɗannan jami’ai na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da rikice-rikice, da badakalar da ke addabar gwamnatin.
Ndume ya kuma yi nuni da wata badakala da ta shafi wata hukumar gwamnati da ake zargin ba ta da inganci, wadda ya ce ta yi aiki har ta samu ofishi a harabar ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Ya yaba wa Shugaba Tinubu kan matakin da ya ɗauka na dakatar da wasu manyan jami’an gwamnati da kuma ba da umarnin kama wanda ake zargin yana gudanar da hukumar.
Sai dai sanatan ya ce har yanzu shugaban bai ɗauki mataki wajen magance matsalar rashin kwarewar wasu jami’an gwamnatinsa ba.
A cewarsa, da akwai masu cikakken kwarewa a mukaman gwamnati, da ba a samu irin wadannan badakaloli da abubuwan kunya ba.
