
Sanata Barau Jibrin yana jawabi a garin Bunkure a yayin ziyarar Jajen
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a Uromi ya kuma ba su tallafin Naira miliyan 16.
Sanatan ya jajantawa iyalan wadanda aka kashe ne a Masallacin At-Taqwa dake Bunkure a ranar Laraba.
A jawabinsa yayin ziyarar Mataimakin Majalisar ya yi musu ta’aziyya da kuma tabbatar musu da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.
“Na zo nan ne domin na yi muku jaje kan wannan mummunan al’amari da ya jawo rasuwar ’yan uwanku 16. Allah Ya Sa Aljanna Firdausi ta zama makomarsu, Ya kuma bai wa waɗanda suka ji rauni lafiya.
“Ba za mu ɗauki hakan da sauƙi ba. Za mu tabbatar cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.” In ji shi.
Aminiya ta rawaito cewa, Sanatan ya kuma sanar da bai wa kowane daga cikin iyalan mamatan kyautar Naira miliyan ɗaya wanda ya kai jimillar Naira miliyan 16.
Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Sheikh Zainul Abidina Auwal, limamin yankin, ya godewa Barau bisa ƙoƙarinsa da yadda ya damu da lamarin.
A yayin ziyarar jajen Sanatan Barau na tare da Ministan Kula da Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da kuma sauran manyan jami’an jam’iyyar APC a jihar.
Mutanen da aka kashe sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure da Kibiya da Rano da kuna Garko a Jihar Kano.