Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance mutum shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin naɗa su a matsayin kwamishinoni a gwamnatinsa.
Waɗanda aka gabatar sun haɗa da Ibrahim Namadi Dala, Mukhtar Ishaq Yakasai, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, Idris Garba Mustapha da Salisu Yusha’u Soja.
Tun a ranar Laraba, 21 ga Oktoba, Shugaban Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya karanta wasiƙar da gwamnan ya aike, inda ya buƙaci majalisar ta tantance tare da amincewa da naɗin mutanen shida.
Matakin na zuwa ne a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na cike guraben kwamishinonin da suka samu bayan sauye-sauyen siyasa a jihar.
Ana jiran matakin majalisar na ƙarshe kan amincewa da naɗin waɗanda aka tantance.
