Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta ce ta gano wasu ƙarin hukumomin bogi guda biyu a yayin da take ci gaba da bincike kan hukumar PFIPC.
Shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis bayan ya miƙa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu rahoton wucin-gadi na binciken a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Aliyu ya ce binciken ya gano cewa ana zargin Adeniyi Matthew Adeyemi ne ya ƙirƙiri waɗannan hukumomin bogi, tare da amfani da giɓin da ke cikin tsarin aiki na wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati wajen gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa binciken ya tabbatar da cewa Adeyemi bai taɓa samun naɗi daga Gwamnatin Tarayya ba, sannan hukumar PFIPC ba ta da wata halastacciyar kafa, domin ba a kafa ta ta kowace doka, umarnin shugaban ƙasa ko wata takardar gwamnati da ta ba ta sahalewar gudanar da aiki ba.
Shugaban ICPC ya ce an miƙa rahoton ne kwanaki 30 cif bayan Shugaba Tinubu ya umarci hukumar da ta gudanar da bincike kan ayyukan PFIPC.
Ya ƙara da cewa binciken ya nuna cewa abin da ake kira Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) ba hukuma ce ta gwamnati ba, kuma ba ta taɓa samun wata halastacciyar kafa daga gwamnatin tarayya ba.
