Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Gwamnan ya ce ranar ’yancin kan ta ba ’yan Najeriya damar yin tunani kan tafiyar ƙasar tun bayan samun ’yancin kai a shekarar 1960, tare da girmama irin sadaukarwar da al’ummomin baya suka yi wajen gina Najeriya.
Ya amince cewa hauhawar tsadar rayuwa da sauran matsalolin tattalin arziki da zamantakewa na ci gaba da jefa iyalai da al’umma cikin matsin lamba, amma ya ce hakan bai kamata ya karya gwiwar ’yan Najeriya ko rage musu fata game da makomar ƙasar ba.
Bala Mohammed ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa, inda ya buƙaci ’yan Najeriya su mutunta juna tare da guje wa rarrabuwar kawuna bisa kabila, addini, siyasa ko wani bambanci.
Ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da mata da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya da tattaunawa a tsakanin al’umma.
Gwamnan ya ce gina ƙasa ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, yana mai cewa kowane ɗan ƙasa na da rawar da zai taka wajen ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
