Ana zargin wasu yara biyar sun rasu sakamakon cutar mashako a cikin kwanaki bakwai, a unguwar Danbare New Layout, dake karamar hukumar Kumbotso a Kano.
Mahaifin yaran malam Ibrahim Yusuf ya ce yaran, maza biyu da mata uku, sun rasu ne tsakanin ranar 1 zuwa 7 ga watan Oktoban da muke ciki, lamarin da ya jefa iyalan cikin jimami tare da haifar da fargabar yiwuwar yaduwar cutar a yankin.
Mahaifin Yusuf, ya bayyana yadda lamarin ya faru, tare da cewa yara shida ne suka kamu da cutar, wanda daya daga ciki ta samu sauki, 5 suka rasu.
A nasa bangaren, Darakta-Janar na Hukumar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano, KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ya ce hukumar za ta gudanar da bincike kan lamarin, yana kuma kira ga jama’a da su kai duk wanda ya fara nuna alamun rashin lafiya zuwa asibiti domin samun kulawa cikin gaggawa.
