Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW) , a dukkan lamuran su, domin neman dacewa a wajen Allah.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin saƙon taya al’ummar Musulmin jihar da Najeriya baki ɗaya murnar Mauludin Annabi Muhammad (SAW).
Gwamna Yusuf ya kuma buƙaci Musulmi su yi amfani da lokacin maulidin wajen nazari tare da koyi da rayuwa, koyarwa da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW), musamman zaman lafiya, adalci, tausayi, gaskiya, haƙuri da juriya.
Gwamnan ya buƙaci iyaye, malamai da dattawan al’umma su ƙara ƙaimi wajen koyar da matasa tarihin rayuwa da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW), zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna tsakanin al’umma mabambanta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yin fatan Musulmi za su gudanar da bukukuwan Mauludi cikin lumana da samun albarka, tare da kira gare su da su ci gaba da addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
