
Aminu Abdullahi Ibrahim
Dalibai biyu da suka wakilci reshen Kano na Ƙungiyar Masana Kimiyyar Chemistry ta Najeriya, CSN, sun samu kyakkyawan sakamako a gasar Chemistry ta ƙasa ta shekarar 2026.
An gudanar da gasar ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, ranar 29 ga Agustan 2026.
Abdussalam Nura, ɗalibi a makarantar Day Science College da ke Kano, ya zo na takwas a matakin ƙasa, sannan ya zama na farko a yankin Arewa maso Yamma.
Haka kuma, abokin karatunsa, Murtala Abba, ya zo na 15 a matakin ƙasa, sannan ya kasance na biyu a yankin Arewa maso Yamma.
Reshen Kano na Ƙungiyar Masana Kimiyyar Chemistry ta Najeriya ya taya daliban biyu, makarantar da suke karatu da kuma duk wadanda suka taimaka wajen samun wannan nasara.
